Babban jami'in tsare tsare na cibiyar fasahar sadarwa da cigaban al'umma ko CITAD Isa Garba yace a watan da ya gabata sun samu kalamun batanci fiye da dari biyar kuma yawancinsu akan kabilanci ne ko addini.
Inji Isa Garba sun samu kalamun batanci 548. Kalamun batanci 210 sun fito ne daga bangaren addini yayinda da 255 suka fito ta bangaren kabilanci. Wato wannan na nuni ke nan kabilanci da addini su ne kan gaba wajen kalamun batanci a Najeriya.
Kalamun batanci ta kowace hanya ka iya kawo kyama ko kiyayya tsakanin al'umma ko ya ingiza wata al'umma walau ta farma wata al'umma ko ta kita. Hakan kuma ka iya kawo yaki ko wani tashin hankali.
Akan irin rawar da shugabannin addini da al'umma zasu iya taka Isa Garba yace dole ne malamai su dinga fadakar da mutane su kaucewa kalamun baanci kamar yadda addini ya koyar. Idan kuma an yi kalamun batanci da sunan addini ko kabila su fito suyi tur dashi.
Ita ma gwamnati, inji Isa Garba dole ne ta dauka babu wani abun da ba nata ba. Ta dauka duk al'umma nata ne. Kada gwamnati ta nuna wariya bisa kabilanci ko addini. Ta ba kowane dan kasa 'yancinsa ko menene ma addininsa ko kabilarsa.
Isa Garba ya kira gwamnati tayi anfani da ofishin fadakarwa tana fadakar da al'ummarta akan hadarin kalamun batanci.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5