Babban sakona a kullum shine mutane su kasance masu tawakali akan duk abinda Allah ya basu su dangana da Allah ne ya basu ba mutum ba, haka kuma su kasance sun kauracewa gadara da fadin rai, inji mawakin reggae David Samson Hassan wanda aka fi sai da David Suazo.
Suazo ya bayyana cewa ya koyi kidan jita a wajen wani mawaki da ake kira brother Raymond London, matashin ya kara da cewa a wasu lokutan jama’a na yi masu kallon marasa aikin yi kuma marasa da’a.
Ku Duba Wannan Ma Amitabh: Labarin Malamin Makaranta Da Ya Kafa Kungiyar Kwallo Da Zauna Gari BanzaDavid ya bayyana cewa yakan fadakar da al’umma cewar waka wata hanya ce ta isar da sako ta yadda zai ratsa zuciyar mutune cikin sauki da annashuwa ba tare da an tursasa su ba, kuma duk a lokaci guda a wa’azantar da su.
Daga karshe matashin ya bayyana cewa “ni mawakin Raggae ne wanda ke isar da sakonni ta hanayar waka tare da nusar da al’umma su zama masu dogaro da kansu a rayuwa ba tare da sun kwaikwayi rayuwar wasu ba”.
“Ni ba kamar sauran mawaka bane domin ina gudanar da ayyukana ne a cikin dakina, na rubuta wakata na karanta tare da kada jita da kaina kuma a hannu guda ina karatu na”.
Your browser doesn’t support HTML5