Mutane Miliyan 4.5 Za Su Fuskanci Matsalar Karancin Abinci a Nijar

Wani yanki na Jamhuriyar Nijar da aka samu karancin ruwan sama a daminar bara

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun ba da sanarwar cewa karancin ruwan saman da aka samu a bara, ya sa al'ummar kasar cikin wani yanayi na matsalar karancin abinci.

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ba da sanarwar cewa mutane fiye da miliyan 4.5 a kasar na fama da karancin abinci a yanzu haka.

Hukumomin sun bayyana hakan ne, bayan da wani bincike ya gano cewa garuruwa da dama na kasar sun yi fama da fari a daminar da ta gabata.

Lamarin da ya sa gwamnatin ta Nijar ta fitar da wannan sanarwa bayan taronta na majalisar ministocinta.

Wannan lamarin har ila yau, ya haddasa karancin ciyawar dabobi.

“Akwai matsala, saboda dabba, idan babu abinci sai dai su mutu," a cewar, Al Mansour Muhammed, sakatare a kungiyar manoma da makiyaya ta KAFAN.

Tuni su ma kungiyoyin fararen hula masu fafutuka suka fara tofa albarkacin bakinsu kan wannan lamari.

“Abu ne da bai kamata ba ace cikin a lokacin da muke a yau, dan adam a kasar Nijar yana fama da karancin abinci.” Inji Malam Jori Ibrahim, mamba a kungiyar Alternative.

Saurari rahoton Sule Mumuni Barma daga Yamai domin karin bayani:

Your browser doesn’t support HTML5

Mutane Miliyan 4.5 Za Su Fuskanci Matsalar Karancin Abinci a Nijar - 2'49"