Mutane Masu Dauke Da Ciwon Shan Inna Ga Sauki Ya Samu

Na'urar Exoskeleton

Wani mutum da ya kamu cutar mutuwar rabin jiki, ya kwashe tsawon lokaci yana jinya. Amma sai ga sauki ya same shi, tun da ya fara amfani da wata jakar baya da ake kira Exoskeleton a turance.

Ita dai wannan jikar tana taimaka mishi samun damar yin tafiya kamar sauran mutane, inda kuma take daukar magana daga kwakwalwar shi, wajen yin tafiya ko kuma tsayawa tare da zama ko tashi.

An dasa wata na’ura a jikin jakar, kana aka hada ta da wasu wayoyi da suke daukan sanarwa daga kwakwalwar matashin mai shekaru 28. A duk lokacin da kwakwalwar shi tayi tunanin yin abu, sai ta sanar da wannan jakar, ita kuma sai ta aiwatar.

An kwashe kimanin shekaru 2 ana gwajin wannan jikar ta wace hanya zata taimaka mishi, da ma sauran mutane masu fama da irin wannan matsalar a fadin duniya. Ita dai wannan na’urar itace ta farko da aka kirkira don irin wannan taimakon a fadin duniya.