Mutane Goma Sha Bakwai Sun Mutu A Wani Tashin Bam A Somalia

Tashin bam a Somalia

A kalla mutane goma 17 suka mutu a wani bam da ya tashi a cikin mota a Mogadishu a jiya Litinin, a wani rahoto da ya tabbatar wa sashen Somali na Muryar Amurka.

Daraktan babban sibiti na Magadishu, Dr Mohammed Yusuf, y ace an kai Karin wasu mutane 28 da suka ji raunuka asibiti.

Fashewar ta auku ne a lokacin da dan kunar bakin waken da ake zargi ya ta da bam din a kofar shiga wani Otel da ke kusa da wata mahada da ake kira K-4 da ake yawan hada-hada a Magadishu.

Shaidu sun fada wa sashen Muryar Amurka na Somali cewa an juya bayan motar ta kalli shingen duba ababen hawa na jami’an tsaro akan hanyar da za ta kai ga filin jirgin saman kasa da kasa na Aden Abdulle da ke babban birnin kasar.
Mayakan Al-Shabab ne su ka dauki alhakin kai harin.