Mazauna yankin Catalonia dake yin adawa da kokarin gwamnatin yankin na ballewa daga kasar Spain, sun yi gangami jiya lahadi a birnin Barcelona.
‘Yan sanda suka ce mutane dubu 350 suka halarci wannan gangami, yayin da wadanda suka shirya shi suka ce mutane har dubu 900 ne suka je. An yi wannan maci cikin lumana, kuma ba a samu wani rahoton tashin hankali ba.
Daya daga cikin ‘yan zanga zangar ya fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa “sun jima suna yin shiru a kan wannan batu.”
A makon jiya, ‘yan yankin Catalonia sun jefa kuri’ar ballewa daga kasar Spain da gagarumin rinjaye. A wannan kuri’ar raba gardamar da gwamnatin Spain ta ce haramtacciya ce, kashi 90 cikin 100 na mutanen yankin sun amince da yankin ya balle, sai dai kasa da kashi hamsin cikin 100 na masu jefa kuri’a ne suka fita a lokacin zaben.
Kuri’unb neman ra’ayoyin jama’a sun sha nuna cewa mafi yawan mutanen yankin Catalonia sun fi son su ci gaba da kasancewa cikin kasar Spain maimakon su balle su kafa kasarsu.