Wata hadakar kungiyoyin agaji na yammacin duniya ta fadi tun farko a jiya Talata cewa adadin mutanen da su ka mutu a garin Khan Sheikhoun da ke lardin Idlib sun kai 100 yayin da kuma wasu 350 su ka dimauta.
Kasar Rasha dai ta fito karara ta nesanta kanta daga wannan harin. Ita ma gwamnatin Siriya ta sha karyata zirgin amfani da makaman guba kan farar hula a tsawon yakin da aka kwashe shekaru 6 ana yi.
Kwamitin Sulhu na majalisar dinkin duniya zai tabo batun wannan harin da aka kai a Khan Sheikhoun a wani zama na gaggawa ranar Laraba da safe.
Daga can kudancin kasar kuma, masu saka ido na kungiyar kare hakkin dan adam a Siriya ta ce mutane akalla 25, galibinsu mata da yara sun halaka jiya Talata a wani harin jirgin sama da aka kai a wurare da dama a gabashin birnin Dimashku.