Mutane 86 Sun Mutu a tagwayen fashewar bom a Turkiya

Gawarwakin mutane an rufe da tuta

A kalla mutane tamanin da shida suka rasu yayinda maitan kuma suka jikkata a tagwayen fashe fashen da suka auku a babbar tashar jirgin kasar Turkiya

Wadansu tagwayen fashe fashe da suka auku a babbar tashar jirgin birnin Ankara yau asabar da asuba, ‘yan sa’oi kafin fara wani gangamin masu goyon bayan Kurdawa, sun yi sanadin mutuwar mutane 86 da kuma jikkata kimanin 200.

Fashe fashen sun auku ne dab da kofar fita tashar jirgin dake lardin Ulus na kasar Turkiya. An hakikanta cewa, an kai harin ne da nufin kashe mutane da dama da aka kyautata zaton zasu halarci gangamin da kungiyoyin kodago da sauran kungiyoyin al’umma suka shirya.

Jami’ai sunce yana yiwuwa adadin wadanda suka rasu ya karu.

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya kushewa harin. Ya kuma sanar da janye duk wadansu ayyuka da yayi niyar gudanarwa cikin kwanaki uku masu zuwa, da nufin maida hankali kan kalubalar tsaro da Turkiya ke fuskanta.