Mutum tamanin-da-biyar sun samu raunuka, bayan da wani jirgin saman fasinja mallakar kamfanin Aeromexico ya fadi a jihar Durango da ke arewacin kasar, amma dai babu wanda ya mutu, kamar yadda gwamna Jose Rosas Aispuro Torres ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Jirgin mai lamba biyu-hudu-uku-daya, ya fadi ne, mintina kadan bayan da ya tashi daga filin jirage na Durango Guadalupe Victoria a jiya Talata, a lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa birnin Mexico.
Gwamna Torres ya fadawa manema labarai cewa, matukin jirgin ya yi kokarin ya katse tafiyar bayan da ya fahimci cewa yanayi ba shi da kyau, amma kuma ya makara.
Rahotanni kan yanayi, sun nuna yadda hadari ya bazu a yankin a lokacin da hadarin ya auku.
Fasinjoji 97 da ma’aikata hudu ne a cikin jirgin mai kirar Embraer 190.