Mutane 8 Sun Mutu A Arangamar Soji da Mahaka Ma’adinai A Ghana

  • VOA Hausa

John Dramani Mahama

A wani al'amari mai matukar bakanta rai, arangamar da ta kaure tsakanin mahaka ma'adinai ba bisa ka'ida ba da jami'an tsaro a Ghana ta yi ajalin takwas daga cikinsu.

Masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba su wajen takwas ne su ka rasu sakamakon arangama da sojoji da ke gadin kamfanin hakar zinare na AngloGold Ashanti a tsakiyar yankin Obuasi na kasar Ghana.

Hajia Fatima, daya daga cikin mahalarta jana’izar mamatan ta ce, "dan'uwa na da nike dogaro da shi kadai na rasa shi. Abin da mu ke bukata shi ne a gudanar da bincike domin ajiye doka mazauninta"

Mutane kimanin takwas ne suka rasa rayukansu a wannan arangama ta tsakanin masu hakar ma'adinai ba bisa ka’ida ba da sojojin da ke gadin kamfanin hakar zinari na AngloGold Ashanti a tsakiyar yankin Obuasi na kasar Ghana .

Arangama tsakanin soji da mahaka ma'adinai a Ghana3: Hotunan jana'izar mamata

A cikin wata sanarwar da rundunar sojan kasar ta fitar ta ce sun yi artabu da masu hakar ma'adinai ba bisa ka’ida ba a ranar Lahadi da dare kuma kusan 60 daga cikinsu na dauke da makamai da suka hada da bindigogi da adduna. Sanarwar ta kara da cewa mahakan sun kutsa kai cikin shingen kamfanin da ke da lasisin hakar zinare ne a ranar Asabar da dare sannan suka bude wuta bayan motar sintirin soji ta korasu.

Sojojin sun ce wannan shi ne ya sa suka mayar da martani domin kare kansu kuma ana cikin haka ne sai bakwai daga cikin masu hakar ma'adinan suka rasu.

An yi wa soja daya jinya bayan harbin bindiga da a ka yi masa.To sai dai akwai wasu da su ka jikkata kana an kwantar da su asibiti.

Arangama tsakanin soji da mahaka ma'adinai a Ghana2

Sanarwar rundunar ta kara da cewa, yayin rikicin, an kona motoci hudu na kamfanin hakar ma'adinai.

Wata sanarwa da ofishin shugaban Ghana John Mahama ya fitar ta ce ya ba da umarnin gudanar da bincike "don tantance yanayin rikicin da kuma tabbatar da cewa an gurfanar da duk wadanda aka samu da laifi".

Ghana, wadda ita ce kan gaba wajen samar da zinari a Afirka, ta dade ta na fama da rikice-rikice tsakanin sojoji da matasa a yankunan da ake hakar ma'adinai, abinda ke barazana ga tsaron kasar tare da tattalin arzikinta.

Tsakanin watan Janairu zuwa Satumban 2024 Ghana ta samu miliyan 316 sakamakon zuba jari daga ketare. Sai dai wadannan rikice-rikicen na barazana ga tattalin arzikin kasar da ma tsaronta saboda duk wata kasa da ke fama da irin wadannan rikice-rikice ba za ta iya jawo masu zuba jari daga kasashen waje ba, a cewar Sheriff Issah Abdul Salam mai sharhi kan alamuran yau da kullum.

Ya kara da cewa, " abin da ke faruwa dinnan ba labari ne mai dadin ji ba. Yanzu da muke bukatar kudade masu yawa mu zuba a cikin tattalin arzikinmu wanda yake karfin kudin na wannan fanni na gwal da diamond da sauransu. Idan ana samun mutane suna kai ma kamfanoni masu hakar ma'adinai da sauransu farmaki hakan zai kori masu zuba jari. Idan wani na so ya zo ya yi hakar ma'adinai, wanda zai kawo mana arziki, a dauki mutane aiki, ba zai yi ba domin yana ganin in ya zo ba zai samu zaman lafiya ba. Saboda haka ya dade wasunmu mu na cewa wadannan masu hakar ma'adinai ba bisa ka’ida ba, banda lalata kasa, suna kuma kawo ‘yan ta'adda a kasa." inji shi.

Arangama tsakanin soji da mahaka ma'adinai a Ghana1

Shin ina mafita? Shariff Issah Abdul Salam ya ce, "ya kamata gwamnati ta dawo da hankalinta wajen abubuwan da ke faruwa a fannin hakar ma'adinai. Ba wai bata ruwa da dazuka kadai ba. Wajen fannin tsaro da kuma miyagun makamai ya kamata ta duba"

Tuni aka tura jami'an tsaro don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a yankin Obuasi dama halin yanzu an rufe wasu makarantu sakamakon rikicin.

Saurari cikakken rahoton Hamza Adams:

Your browser doesn’t support HTML5

RAHOTON RIKICI TSAKANIN MASU HAKAR MA'ADINAI DA SOJOJI.mp3