Kasar Indiya ta bada rahoton samun sabbin kamuwa da cutar corona wajen 78,761 cikin sa’o’i 24 a yau dinnan Lahadi, wanda a duniya baki daya, shi ne adadi mafi yawa da aka taba gani ckin kwana guda tun daga farkon annobar, a yayin da kuma kasar ke cigaba da bude harkokin tattalin arzikinta.
Wannan ce rana ta hudu a jere da Indiya ta samu sabbin kamuwa da cutar sama da dubu 75 cikin kwana daya.
A yanzu, har a harkokin addinai ana daukar matakan kandagarki a Indiya game da cutar corona.
Indiya mai yawan jama’a biliyan 1.4; da yawan masu dauke da cutar miliyan 3.5 da wadanda cutar ta kashe kuma sama da dubu 63, ita ce ta uku a yawan masu dauke da cutar ta COVID-19 a duniya, bayan Amurka da Brazil.
A wasu biranen kasashen Turai da dama, jiya Asabar an yi ta zanga-zangar nuna rashin amincewa da tsauraran matakan hana yaduwar cutar da aka dauka tun bayan bullar cutar.