Mutane 700 Suke Mutuwa Kullum Yanzu Haka A Birnin Moscow

Hukumomin lafiya na kasar Rasha sun ce yawan wadanda ke mutuwa a babban birnin kasar ya ninku daga 360 zuwa 380 da aka saba gani a sanadin hayaki da hazo mai guba da suka turnuke samaniyar birnin.

Wani jami’in kiwon lafiya na kasar Rasha ya ce yawan mutanen dake mutuwa a Moscow yayi kusan ninkuwa zuwa 700 a kowace rana, a yayin da babban birnin na Rasha ya shiga mako na uku a cikin zafi mai tsananin gaske da kuma hayaki da hazo mai guba daga wutar dajin dake ci a kewayen birnin.

Babban jami’in kiwon lafiya na birnin Moscow, Andrei Seltsovsky, ya fada litinin cewa adadin mutanen dake mutuwar ya karu ne daga 360 zuwa 380 da aka saba gani kullum kafin wannan lokacin. An ce wasu dakunan ajiye gawarwaki na birnin sun cika sun batse.

A ranakun asabar da lahadi yawan iska mai guba ta Carbon Monoxide da wasunsu dake cikin iskar shaka ta Moscow, sun ninka wanda bil Adama ya kamata ya shaka kusan sau 7. A jiya litinin, yawan gubar dake cikin iskar shakar ta ragu zuwa ninki biyu ko uku kan adadin da ya kamata dan adam ya shaka.

Hukumar kula da yanayi ta kasar Rasha ta ce zafin dake addabar Moscow da wasu sassan kasar ya yi muni fiye da kowane lokaci a tarihin kasar. Zafin da ake fama da shi a birnin na Moscow ya kan kai kimanin awu 38 a ma’aunin Celsius, maimakon awu 24 da aka saba gani idan ana zafi.

Haka kuma, fari mai muni ya lalata alkamar da aka shuka a kasar, ya kuma sanya farashin alkama ya tashi a kasuwannin duniya. Rasha tana daya daga cikin manyan masu samar da alkama ga sauran kasashen duniya.