Mutum Biyar Sun Mutu A Wata Fashewa A Jihar Sokoto

Wata fashewar tukunyar gas a Sokoto

‘Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin da ka iya zama sanadin salwantar rayuka baya ga matsalar rashin tsaro da ta dabaibaice kasar.

A jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya da tsakiyar ranar yau ne wata tukunyar gas wadda masu aikin walda ke amfani da ita ta fashe inda ta hallaka akalla mutane biyar ta kuma jikkata wasu masu yawa.

Yankin Isa da ke gabashin jihar Sakkwato ya jima ya na fama da matsalar rashin tsaro, inda kauyuka da dama su ka yi kaura zuwa cikin hedikwatar karamar hukumar inda nan ne kawai ake samun dan sauki.

Fashewar Tukunyar Gas a Sokoto

A cikin garin na Isa wanda nan ne hedikwatar karamar hukumar aka samu fashewar tukunyar gas wadda kuma ta hallaka mutanen da ke kusa da inda ta fashe, kamar yadda wani wanda ya gani da idonsa ya shaida min.

Hakama na zanta da wani dan garin wanda ya Isa gurin jin kadan bayan aukuwar lamarin.

Na tuntubi kantoman karamar hukumar mulkin Abubakar Yusuf Dan Ali ya ce baya Sokoto, ya yi tafiya, amma an kira shi an shaida masa kuma ya na kan tattara bayanan yadda abin ya kasance.

Na kuma tuntubi jami'an tsaro inda kakakin rundunar ‘yan sanda a Sakkwato DSP Sanusi Abubakar ya ce za su bincika.

Wannan ba shi he karo na farko ba da ake samun irin wannan matsala a Najeriya tare da jan hankulan jama'a akan su rika daukar matakan kauce wa faruwar irin hakan.

Your browser doesn’t support HTML5

Mutane 5 Sun Mutu a Wata Fashewa 3.mp3