Kungiyar sa ido kan hakkokin dan adam dake kasar ta ce 'yan kunar bakin wake da yawa sun tashi bama-bamai a kusa da hedkwatar tsaro ta jihar da kuma ma’aikatar tsaro ta soji.
Tuni dai kungiyar Al Qaeda ta dauki alhakin wannan hari, inda ta ce 'yan kunar bakin wake biyar ne suka far wa yankin na Homs dake cike da tsaro.
Birnin ya kasance karkashin mulkin gwamnati kusan tsahon shekaru uku.
A jiya juma’a a arewacin Syria, 'yan kunar bakin wake biyu suka tashi bam a cikin mota wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 65, ciki har da fararen hula da mayakan 'yan tawaye da kuma sojojin Turkiya guda biyu.
Harin na kusa da Al-Bab ya zo ne bayan dakarun Turkiya dake marawa 'yan tawaye baya suka kwace kusan duk wasu wurare masu muhimmanci daga hannun 'yan ISIS.