Kimanin kwanaki 33 kenan da bala'in ambaliyar ruwa ta lalata dubban gidaje tare da raba dubunnan mutane da muhallansu a garin Gummi da ke jihar Zamfara, sai kuma gashi a yau akalla mutane 35 sun bace bayan da aka samu hatsarin wasu kwale-kwale biyu da su ka yi karo da juna a cikin gulbin garin Gummi a mashayar Tsohuwar Kasuwa.
Lamarin ya faru ne a lokacin da wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji sama da 40, yawancinsu manoma, da ke kan hanyar zuwa gonakinsu, ya fara tangal tangaka a cikin ruwan sakamakon matsanancin lodin da aka yi ma shi, hakan ya sa direban wani kwale kwale ya yi yunkurin ba su agaji sai su ka yi taho mu gama da juna, inda duka jiragen biyu suka nutse a cikin ruwan.
A cewar Bello Abubakar, mataimakin shugaban masu gudanar da sana’ar tukin kwale-kwale na jihar Zamfara, an gargadi matukin jirgin akan ya rage yawan mutanen ke ke cikin jirgin.
"Jirgin ruwan ya taso ne a tsakiyar tafiya, kuma wani ma'aikacin jirgin ya yi yunkurin taimakawa, amma abin takaici, kwale-kwalen biyu sun yi karo da juna, kuma dukkansu sun nutse," in ji Abubakar.
Ya ce ya zuwa yanzu dai, masu aikin ceto sun yi nasarar ceto mutane bakwai ne kawai, inda ya ce har yanzu ba a gano adadin mutane 35 ba.
Shaidun gani da ido da suka hada da Zayyanu Aliyu, sun bayyana cewa a cikin fasinjojin har da maza da mata da kuma yara kanana. "An gargade su, amma sun ki fita daga cikin jirgin da ya yi lodi fiye da kima," in ji Aliyu.
Shi kuwa Murtala Sa’idu wanda ya tsallake rijiya da baya ya tsira da ransa bayan nutsewar kwale kwalen ya ce sun shiga tashin hankali a lokacin da suka nutse kafin daga bisani a samu nasarar ceto su”
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara CP Shehu Muhammad Dalijan wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da suka hada da askarawan Zamfara da ’yan banga suna wurin da lamarin ya faru suna ba da kariya da goyon bayan aikin ceto.
“Tabbas wannan mummunan lamarin ya faru, amma yanzu haka mu na nan ana bakin kokarin ganin an ceto sauran mutanen, domin yanzu haka jami’an yan sanda da sauran abokan aiki suna a wurin da lamarin ya faru domin bada tsaro da taimakawa wajen ceto Mutanen.
Injiniya Bala Muhammad Bello, kodinetan hukumar Kula da Hanyoyin Ruwan ta Najeriya mai kula da jihohin Sokoto da Zamfara, ya nuna rashin jin dadinsa kan lamarin, saboda a cewar shi matakin kwale kwalen ya ki daukar shawarar da aka ba shi na rage yawan mutanen da ke cikin jirgin.
“Shugaban hukumar Kula da Hanyoyin ruwa ta Nigeria Dakta Bola Oyebamiji ya bada umurnin a tura wata tawaga daga hukumar domin aje a duba lamarin a Dauki matakai tare da bada shawarwari don kauce wa sake faruwar hakan,” inji Injiniya Bala.
Ya zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto, masu aikin agaji da kwararru na cikin gida na ci gaba da bincike a cikin kogin don ceto mutanen da suka bata a ciki.
Your browser doesn’t support HTML5