Rundunan 'yan Sandan jihar Adamawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya, sun gabatarwa wa manema labarai wasu mutane 32 da ake zargin masu garkuwa da mutane da Satan shanu ne a shalkwatar hukumar 'yan Sandan a birnin Jimeta a fadar mulkin jihar ta adamawa.
An same su da kudi fiye da naira miliyon daya da wasu motoci guda hudu da bindiga kirar AK 47 guda biyar da wasu bindigogin kirar hannu guda ashirin da daya (21)
Khakakin Rudunar 'yan Sandan jihar ta Adamawa SP Sulaiman Yaya Nguroje ya yiwa manema labarai karin haske game da mutanen da ake zargi da aikata manyan laifuka da suka hada da garkuwa da mutane don nema kudin fansa a jihar da kuma masu satan shanu.
Daya daga cikin wandanda ake zargi da garkuwa da mutane a jihar Adamawan, Aliyu Muhammad ya ce wannan shine karon farko da ya fara wannan mummunan aiki na garkuwa da mutane amma kuma dubun shi ya cika.
Shi kuma Aliyu Buba daga karamar hukumar Fufore a jihar Adamawar, ya ce sau uku yana garkuwa da mutane a yankin Mayo Ballwa da kuma karamar hukumar Yola ta Kudu, ya ce duk da cewa suna karbar kudin fansa da yawa, amma ba a bashi wani kaso mai tsaoka.
Sai kuma, Ibrahim Adamu wanda aka kama shi cikin wadanda ake zargin, sai dai Ibrahim ya ce yanzu shekaru biyu kenan yayi hannun riga da wannan muganyar aiki. Yace a baya, ya taba yin garkuwa da mutane sau biyu amma yanzu ya tuba.
A saurari rahoton Lado Salisu Garba:
Your browser doesn’t support HTML5