Bayan tashin bam-bamai a kasuwar Madagali dake a jahar Adamawa, kakakin runduna ta 23 dake garin Mubi Majo Badare, ya tabbatar da cewa mutane 30 ne suka rasa rayukansu wasu sama da tamanin suka jikkata kuma ke Asibitin Michika da Madagali.
Shugaban karamar hukumar Madagali Mallam Yusuf Mohammed, wanda ya tabbatar da tashin bama-baman ya ce cikin 'yan kwanakin da suka gabata an sha kaiwa kauyukan hare-haren dauki ‘dai ‘dai da kuma sace mutane.
An dai sami tashin bama-baman guda biyu a kasuwar ta Madagali a sashen ‘yan kasuwar Buhuna da na Gwanjo, wadda ake tuhuma wasu mata ‘yan kunar bakin wake guda biyu ne suka tayar da su.
Tashin bama bamai na baya bayan nan zai iya jefa al’ummar yankin cikin fargaba, musamman wadanda ke zaune a wasu sassa na kasar dake da niyyar komawa gida bikin Kirsimeti nan da makonni masu zuwa.
Tuni dai rundunar soja da ke Yola fadar jiha ta aika da ayarin dakarunta da ‘yan sandan jaha don tabbatar an shawo kan abin da ka iya biyo baya.
Domin karin bayani saurari rahotan Sunusi Adamu.
Your browser doesn’t support HTML5