Tagwayen hare haren bam da aka boye cikin motoci, sun kashe mutane ashirin da bakwai da raunana wasu mutane dari da arba’in, yawancinsu farar hula a Damascus baban birnin Syria.
Kafofin yada labarun kasar, sunce bama baman sun tashi ne yan mintoci a tsakani a kusa da wani ofishin yan sanda da cibiyar lekan asiri a birnin Damascus.
Gidan talibijin na kasar ya nuna hotunan vidiyon wuraren da al’amarin ya faru da suka nuna hayakin na tashi da karafan da suka mokade daga wani gini da harin ya shafa da kuma gawarwarkin mutane da suka yi raga raga, babu kyawun gani. Haka kuma gidan talibijin din ya zanta da mutane da dama. Yawancin mutanen da aka zanta dasu, sun dorawa shugabanin yankin Gulf da gidajen talibijin na Larabawa da laifin tsokono fitina a kasar.
Nan da nan babu wata kungiyar data bigi kirji tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai hare haren, to amma jami’an Syria sun dorawa yan ta’ada laifi, suna masu fadin cewa wasu masu harin kunar bakin wake guda biyu sun tarwatsa kasu kusa da gine ginen gwamnati.
An dai kai wadannan hare hare ne a yayinda masanan Majalisar Dinkin Duniya suke shirye shiryen kai ziyara Syria domin tattauna yiwuwar tura masu lura na kasa da kasa, a zaman wani bangare na yunkurin da ake yin a magance mmumunar tarzoma da murkushe yan tawaye da gwamnatin kasar keyi.