Mutane akalla 26, ciki har da fararen hula, sun halaka a wani harin da wasu ‘yan bindiga wadanda ba a san ko su waye ba su ka kai sansanin Rundunar Kai Daukin Gaggawa (RSF) da ke garin Kadugli na jar Kordofan ta Kudu.
Kwamandan rundunar ta RSF Janar Hamdan Dagalo ya yi Allah wadai da wannan harin.
Hukumomin garin na Kadugli sun ce wasu mutane ne saye da kakin soji kuma dauke da bindigogi su ka kai hari kan sansanin na RSF.
Baya ga wadanda su ka mutu din kuma wasu kuma guda 19 sun samu raunuka kuma an dauke su da jirgin sama zuwa Khartoum saboda a masu jinya, a cewar Manjo-Janar Rasheed Abdulhameed Ismael, Gwamnan soji na jahar ta Kordofan ta Kudu.
Babu dai wanda aka kama zuwa lokacin hada wannan rahoton, kuma har yanzu ba a san ko su waye ‘yan bindigar ba, to amma an ce sun iso ne a wasu motoci hudu na Land Rover.
Janar Dagalo, wani mamban majalisar kolin kasar Sudan, ya kira wannan harin aika-aikar siyasa. Ya zargi wasu da bai bayyana sunayensu ba da kokarin haddasa husuma a kasar ta wajen kawo rigimar kabilanci tsakanin mazauna wurin da kuma haddasa rigima tsakanin rundunarsa ta RSF da sojojin Sudan.