Maza da mata da yara,wadanda suka suka garzya inda ta kifen domin kwasar ganima. Hukumomin kasar suka ce fiye da mutane 100 ne suka jikkata a fashewar, kuma da yawa daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.
Tankar tana taso ne daga birnin karachi mai tashar jiragen ruwa dake kudancin kasar, zuwa Lahore hedkwatar lardin Punjab, sa'ilinda motar ta kubucewa matukinta. Sanarwar da aka bayar ta na'urori masu kara sauti a wani masallaci cewa wata tankar mai tayi hadari har mai yana yoyo, yasa mnazauna kauyuka da suke kusa suka dunguma zuwa wurin domin kwasar mai. A lokacin ne kuma motar tayi bindiga ta apka kan wadanda suke wurin da kuma motoci da suke kusa.
Man fetur abune da yake da tasiri a Pakistan, duk d a hadari dake tattare da shi, tunanin samunsa kyauta yana sa mutane su mance da hadarin dake tattare da kwasar ganima.
Babu tabbas kan abunda yasa tankar tayi bindiga. Amma Yansanda dake yankin sun ce matukin ya tsira da ransa kuma tuni aka kama shi.