Wani mummunan farmakin ta’addanci da aka kai kan iyakar kasashen Kenya da Somalia ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 12, a cewar wasu jami’an kasar Kenya.
WASHINGTON, DC —
Job Boronjo, wanda shine kwamandan ma’aikatan tsaron yankin Mandera, yace mayakan al-Shebab na Somalia ne suka kai wannan farmakin akan gidan sauke baki na Bisharo, inda suka yi anfani da gurnetoci wajen kai harin nasu.
Ba da bata lokaci ba kungiyar al-Shebab tayi sauri ta dauki alhakin cinna wannan ta’asar a sanarwar da ta bayar kan shafinta na “telegram”, inda kuma tace ta auna abinda ta kira “ma’aikata Kiristoci” ne.
Wannan harin da aka kai jiya Talata dai ci gaba ne da iri-irensa da al-Shebab ta jima tana kaiwa kan yankunan kan iyakar tun shekarar 2011.