Karancin ruwa na haddasa bakin cututtuka. Abin da ke faruwa kenan a Somaliya, inda ake fama da wata cuta mai zuwa lokacin fari
WASHINGTON, D.C. —
Jami'an Gwamnatin Somaliya sun ce mutane sama da 110, akasari mata da yara, sun mutu sanadiyyar wata cutar da ake daukawa a ruwa cikin sa'o'i 48, sanadiyyar fama da rashin ruwa da ake cigaba da yi a kasar.
Da ya ke hira da manema labarai jiya Asabar a Mogadishu, sabon Fira Ministan Somaliya Hassan Ali Khaire, ya bayyana mutuwar mutanen, wanda shi ne adadin farko na hukuma tun bayan mummunan farin da aka kwashe watanni ana yi.
Ya yi kira ga Somaliyawa da al'ummar duniya da su hada gwiwa wajen daukar mataki