Mutane 11 Sun Mutu A Sabuwar Zanga-Zanga A Sudan

Wani rahoto daga kasar Sudan yace kimanin mutane 11 suka mutu a wata zanga-zangar neman maida kasar akan tafarkin mulkin farar hula.

‘Yan sanada sun harba barkonon tsohuwa akan dubban masu zanga-zangar da aka yi a ranar Lahadi da ta gabata a babban birnin Khartoum, da wasu sassa a kasar.

Daga nan Washington, kuma gwamnatin Amurka ta yi Allah wadai da irin karfin da aka nuna akan masu zanga-zangar.

A halin yanzu kuma, yayinda masu zanga-zangar ke ci gaba da matsin lamba akan sojan da suka tumbuke tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir, da su hanzarta maida kasar akan tafarkin demokradiya, akwai alamar cewa kungiyoyin kishin Islama na fuskantar kalubale wajen samun bakin magana akan makomar kasar.

Wadannan kungiyoyin na ‘yan kishin Islama sun taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa al-Bashir darewa kan karagar mulki.

Wannan yasa ake ganin halin da aka shiga yanzu a Sudan ba zai taimake su samun shiga a cikin rukunin kungiyoyin dake sahun gaba wajen shata sabuwar makomar kasar ba.