Musulmin Indonesia tun cikin watan Maris suka kaucewa alkibla

Mecca.

Majalisar Malaman Indonisiya, tace ta yi kuskure wajen gwadawa masallata alkibla.

Babbar hukumar kula da harkokin adddinin Islama a Indonisiya ta ce da jumawa musulmin kasar basa fuskantar alkibla dai dai.

Majalisar malaman kasar, litinin din nan ce, ta fito fili t ace ta yi kuskure tun cikin watan Maris, da ta auna alkiblar ta yammacin kasar.

Shugaban majalisar malaman Ma’aruf Amin, yace bayan tuntubar masana taswirar Duniya, da malaman taurari, hakan ya nuna cewa musulman Indonisiya, kudancin Somalia da Kenya suke fuskanta idan suka zo Sallah, ba makka ba,wanda yake kilomita dubu daya dari shida daga can arewacin kassar.

Amin ya bukaci musulmin su dan su karkato arewaci, idan za su yi sallah. Yace wan nan kuskure ba yana nufin sallarsu ba ta karbu ba, yace Allah yasan ‘yan Adam suna kuskure. Koda shike dai Indonisiya ba bin tafarkin gama mulki da harkar addini, ita ce kasa da tafi ko wacce yawan musulmi a Duniya,kusan milyan 243.