Kamar koina a fadin duniya, a birnin Konni, an gudanar da bikin Kiristimeti, ranar tunawa da haihuwar Annabi Isa A S (Yesu Amasihu).
Ladanin majami’ar Katolika, dake birnin Konni, Malam Arzuka yace babbar mahimmanci ranar kiristimeti, bashi da iyaka amma daya daga ciki shine tunawa da mai ceton duniya Yesu Almasihu.
Domin shagalin wannan ranar Musulmai, sun taya ‘yan uwansu Kiristoci shan shagali, kamar yadda Malama Rakiya ta Majami’ar Katolika, dake birnin Konni, ta shedawa muryar Amurka.
A bangaren Musulmi, Dan Liman, yace da Kiristoci da jama’ar Musulmi uy7ana fatar Allah ya bada zaman lafiya, a kasashen duniya baki daya da kuma fatan alheri,saboda Musulmi, da Kirista duk ‘yan uwan juna ne.
Your browser doesn’t support HTML5