Idan dai ba’a mance ba, a ranar 19 ga watan Janairun da ya wuce ne dai shugaba Buhari ya tafi hutu tare da ganin likita a Birtaniya, to amma kuma daga bisani sai shugaba Buharin ya sake aika wa Majalisar Dokokin kasar takardar neman tsawaita hutun da zummar kammala gwaje-gwajen lafiyarsa.
Tun wannan lokacin ne aka fara gudanar da addu’o’i a Majami’ai da Masallatai don nema wa shugaban lafiya.
Da suke gabatar da addu’o’in Evangelist John Adamu da Sheikh Aliyu Babando da kuma wakilin kungiyar CAN, Rev. Baba Yerima, sun yi addu’ar neman Allah ya baiwa shugaban kasa lafiya da kuma kawo daidaito a jihar Taraba.
Shima da yake jawabinsa a wajen gangamin addu’ar Galadiman Muri, Alhaji Tukur Abba Tukur, ya yaba da yadda jama’a suka fito don gudanar da wannan addu’a
Shi kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC a jihar, Hassan Jika Ardo, yace ya zama dole ‘yan Najeriya su tashi tsaye don yiwa shugaba Buhari addu’a, idan aka yi la’akari da irin nasarar da aka fara samu kasar.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5