Shugaban Musulmai tare da na Kiristoci suka hallara inda suka yi adduo'i na mausamman suna yiwa Allah godiya da dawo da shugaban kasa Buhari tare da yi masa fatan tsawon rai cikin koshin lafiya.
Taron ya samu halartar 'yan siyasa da kungiyoyi daban daban. Shugaban taron Alhaji Abu Muazu Yariman Kashere ya gargadi su matasan kasar da su yi koyi da halayan Buhari. Yana mai cewa abun da shugaban ya shimfida masu shi ne gaskiya da rikon amana da tausayin talakawa.
Yace kullum safiya da lokacin da aka yi sallah a dinga tunawa da shugaban kasa. Kiristoci kuma yayinda suka je mijami'unsu sun dinga yiwa shugaban addu'a.
Alhaji Bala Timka, jigo a jam'iyyar PDP dake mulkin jihar yace gwamnan jihar Hassan Dan Kwambo ya bada umurnin a dinga yin addu'o'i a masallatai da mijami'u domin neman wa shugaban kasa lafiya.
Matasan Gombe sun yaba da taron da fatan Allah ya ba shugaban kasar cikakkiyar lafiyar jiki.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5