Kungiyar kwallon kafa ta Wikki Toutist ta tabbatar da dawo da Mustapha Ibrahim a matsayin dan wasanta da zai fafata mata a kakar 2019/20.
Dan wasan na baya gefen dama wanda a kakar shekarar da ta gabata na 2017/18, ya koma kulob din Gombe United daga Wikki inda ya shafe shekara daya kacal.
Mustapha ya rike mukamin jagoran 'yan wasan Wikki Tourist (Captain) na tsawon shekaru uku da suka wuce, ya kuma buga wa tawagar 'yan wasan kwallon kafa ta 'yan kasa da shekaru 17, Golden Eaglet a shekarun baya.
Dan wasan ya nuna jindadinsa na dawowa tsohowar Kungiyarsa, yadda zai fafata mata a kakar wasan 2019/20.
Ya kuma bayyana cewa babban burin duk wani dan wasa, shine ya ga kungiyar sa ta samu nasarar buga gasar Continental, domin wakiltar kasarsa a wasanni Afirka da CAF take shiryawa, don haka yace zai bada dukkannin iya warsa domin Wikki ta cigaba.
Kungiyar ta Wikki Tourist, zata fara kakar wasan bana na 2019/20 ranar Lahadi 3 ga watan Nowamba 2019, tsakanita da kulob din Jigawa United wacce ta hauro gasar Firimiyar Najeriya.