Attajiri Elon Musk ya bada gudunmowar kusan dala miliyan 75 ga kwamitin harkokin siyasar daya kirkira domin tallafawa yakin neman zaben shugaban kasar Amurka na Donald Trump, a cewar rahotannin da aka shigar da yammacin jiya Talata, abinda ke nuni da karin goyon bayan mamallakin kamfanin Tesla ga tafarkin jam’iyyar Republican.
Musk, mutumin da aka kiyasta cewa yafi kowa kudi a duniya, yana cigaba da taka rawa ta zahiri a yakin neman zaben Trump, inda ya raka shi har kan dandamali a wani gangamin baya-bayan nan a Pennsylvania sannan yana yawan sukar abokiyar hamayyarsa ta jam’iyyar Democrat, Kamala Harris, a kafafen sada zumunta.
Kwamitin harkokin siyasar da musk ya kafa a Amurka (PAC) ya tarawa yakin neman zaben trump dala miliyan 74.95 a tsakanin 1 ga watan Yuli da 30 ga watan Satumbar da ya gabata, a cewar bayanan hukumar zaben tarayyar kasar.
Harris da Trump na tafiya kai da kai a tsaren neman shiga fadar White House, a cewar zabubbukan jin ra’ayi.