Masana tsaro a Najeriya na ci gaba da bayyana damuwarsu kan irin salon yarjejeniyar da gwamnatin kasar ke kullawa da mayakan Boko Haram.
Kusan yawancin tsofaffin hafsoshin sojan Najeriya, na adawa da irin salon sasantarwar da gwamnatin kasar ke yi da mayakan Boko Haram, inda a baya aka sako wasu kwamandojijin mayakan kungiyar da aka yi musayarsu da wasu ‘yan matan Chibok.
Tsohon hafsa a hukumar leken asirin sojan Najeriya, Aliko El-Rashid Harun, yace lokacin da aka yi musayar ‘yan matan chibok su 27 akwai batun cewa gwamnati ta baiwa ‘yan Boko Haram makuden kudade, wanda hakan yayi sanadiyar tashin hankali musamman a Maiduguri da Yola da sauran garuruwa a arewa maso gabashin Najeriya.
Haka kuma lokacin da aka yi musayar ‘yan matan Chibok 82, inda aka saki kwamandojin boko Haram guda biyar. A kasa da kwanaki biyu ‘daya daga cikin kwamandan ya fitar da hotan bidiyo yana mai cewa yanzu ne lokacin da Najeriya zata fara ganin tashin hankali.
Cikin wannan makon ne kungiyar Boko Haram ta fitar da wani sabon bidiyo da ke nuna yadda sukayi garkuwa da wasu mata bayan wani kwantan bauna da suka yi wa motar ‘yan sanda a hanyar Dambua dake jihar Borno.
Anga matan cikin bidiyon na rokon gwamnatin Najeriya da ta karbo su kamar yadda ta karbo ‘yan matan Chibok.
Kamar yadda tsohon gwamnan mulkin soja a jihar Kano, kanal Aminu Isa Kwantagora, irin wannan musayar na da matsala, domin ta haka ne suke amfani wajen samun kudin da zasu sayi abinci da makamai wajen gudanar da ayyukan ta’addanci.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5