Muryar Amurka Za Ta Bude Ofishin Yanki A Kano

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje tare da Shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha Sokoto.

Sashen Hausa na gidan rediyon Muryar Amurka zai bude ofis a birnin Kano, da zai kula da yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Dangane da haka ne shugaban sashen Aliyu Mustapha Sokoto ya kai ziyara a Kanon, domin tantance yadda al’amuran kafa ofishin zasu kasance, inda kuma ya ziyarci gwamnan jihar ta Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Shugaban Sashen Hausa Na Muryar Amurka Aliyu Mustapha Sokoto

Aliyu Mustapha ya shaida wa gwamnan cewa hukumar gudanarwar gidan rediyon na Muryar Amurka ta yanke shawarar kafa ofishin ne bisa la'akari da muhimmancin birnin na Kano ga kasar Hausa da duniya baki daya.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje wanda ke cike da annashuwa dangane da wannan hobbasa ta Muryar Amurka, ya ce, yunkurin ya yi daidai da matsayin Kano na Jalla babbar Hausa.

Ganduje ya ci gaba da cewa "idan kun bude tasha a nan Kano tamkar kun bude ta ne ga dukkan Najeriya da sauran kasashe makwabtanta".

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje tare da Shugaban Sashen Hausa na Muryar Amurka, Aliyu Mustapha Sokoto.

A kan haka gwamnan ya yi alkawarin ba da cikakken goyon baya da hadin kai domin cimma nasarar wannan aiki.

Shi ma Sarkin Bichi, mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero wanda ya yi digiri a fannin aikin jarida da yada labarai shekaru da dama da suka shude, ya ce tsare-tsaren kafa ofishin shiyya da Muryar Amurka ke yi a Kano abu ne da ya dace.

Bayan kafuwarsa, ofishin na Muryar Amurka na Kano zai kula da harkokin aika rahotanni da tsara shirye-shirye na Radiyo da talabijin zuwa birnin Washington DC game da al’amuran da ke faruwa a jihohin Kano, Jigawa, Kaduna, Katsina, Sokoto, Zamfara da kuma Kebbi.

Ga cikakken rahoton daga Mahmud Ibrahim Kwari.

Your browser doesn’t support HTML5

VOA ZATA BUDE OFFICE A KANO