Yarjejeniyar na zuwa biyo bayan fayafayan bidiyo wadanda kungiyar Boko Haram kanta ta nada kuma Muryar Amurka ta yada ta radiyo da talabijan domin fadakar da jama’a ayukan kungiyar wadanda ba su da alaka da addinin Musulunci kuma ba Musulunci ba ne inji babban editan sashen Hausa na Muryar Amurka Alhaji Aliyu Mustaphan Sakkwato.
Ya ce wannan na daga kokarin da Muryar Amurka ke yi na bada nata gudummawa wajen karfafa lamuran da suka shafi harkokin tsaro, sha’anin lafiya, noma da samar da zaman lafiya mai dorewa don haka ne ma ya bukaci kafofin labaran su taimaka wajen yayata shi.
Janar Manajan gidan talabijan na jihar Adamawa Alhaji Yusuf Nadabo Usman ya bayyana yarjejeniyar da cewa faduwa ce ta zo daidai da zama a lokacin da kasar Najeriya ke fama da radadin matsin tattalin arziki, lamarin da ya ce yana shafar kafofin yada labarai mallakar gwamnati ta fannin kayan aiki da horar da ma’aikata.
A daya bangaren inji mukaddashin manajin darakta na kafar labarai na Gotel Alhaji Mohammed El-Yakub ya shaidawa Murya Amurka cewa za a samu muhimman sauye-sauye ta fuskar tsara shirye shiryensu na fadakarwa da zarar yarjejeniyar ta soma aiki.
Da yake bayani kan tasirin wannan yarjejeniyar ta fuskar tsaro shugaban sashen labarai na gidan radiyo na Fombina a Yola mallakar gwamnatin tarayya Malam Bamanga Abdullahi Gombi ya ce wannan ita ce hanya mafi sauki na idar da sakonnin zaman lafiya a lunguna da kauyuka.
Wannan ziyarar ta baiwa babban editan sashen Hausa Alhaji Aliyu Mustapha Sakkwato samar masa wata damar a saduwa fuska da fuska da wadanda ke baiwa shirin da yake gabatarwa a jihar Adamawa.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5