Har Yanzu Mune Cikakkun Shuwagabani

Kungiyar shugabanin kananan hukumomi reshen jihar Filato, ta zargi Gwamnan jihar Simon Lalung, da yiwa dokar kasa karan tsaye baya da ya kori shuwagabanin kananan hukumomi daga mukamansu.

A wani taro manema labarai da ‘yayan kungiyar suka kira sun bayyana cewa jama’a ne suka zabe su dan haka Gwamna ba shida hurumin da zai sauke su daga mukamansu.

Shugaban karamar hukumar Mungu, Mr. Caleb Mutfwang, kuma sakataren kungiyar shugabanin kananan hukumomi a jihar yace “ mune har yanzu cikakkun shuwagabanin kananan hukumomin mu masu cikakken iko da aka zaba shekara daya da ya wuce kuma zaman mu a ofis yakamata ya ci gaba har shekarar 2017, zamu bi maganar daki daki har a samu sulhu ta fannin kotu.”

Wani lauya mai zaman kansa Lauyi Balkantu, yace” a bisa doka idan shugabanin kanana hukumomi zaben su akayi to Gwamna bashi da izini ya sauke su, idan dai zabe akayi to masu saukewa sai masu zaben.”