Shugaban kasa Muhammad Buhari ya ta'allaka nasarar da yace ana samu ga gagarumin shirin samar da kayan aiki na zamani ga mayakan kasar.
Najeriya ta kwashe shekaru cikin halin rashin tsaro wanda yayi sanadiyar salwantar rayukan jama'a da dukiyoyin jama'a da dama, wanda gwamnatin kasar ta jima tana fafatukar magancewa.
Sai dai shugaban kasar Muhammad Buhari yace gwamnatin sa ta yi rawar gani wajen karya lagon ‘yan ta'adda kuma tana kan kokarin an magance matsalolin ta hanyar samar da ingatattun kayan aiki na zamani ga mayakan kasar.
Yace za'a yi shirin na musamman domin bude sashen kula , tashi da saukar jiragen sama na rundunar sojin kasa, inda yace an yi tanadi a cikin kasafin kudin 2023 domin haka. Wannan shirin na zamanantar da aikin sojin zai samu gagarumar kulawa. Haka kuma ana kokarin bunkasa sashen kula da sarrafa kayayyaki na soji, yace yana mai yakinin cewa , ba da jama’a ba za'a samu nasarar wannan kudurin wanda zai kara mayar da rundunar sojin mai dogaro da kanta wajen samar da abubuwan da ake bukata ga samar da tsaro.”
Yanzu haka dai akwai mayakan kasar da ke fafatawa da ‘yan ta'adda a karkashin shiraruwa da dama wadanda babban hafsan mayakan kasar Lt. Gen Faruk Yahaya yace kwalliya na biyan kudin sabulu saboda ingatattun shiraruwan samar da kayan aiki da inganta jin dadin jami'an sojin.
“Yace hakan ya kara kuzarin jami'an soji dake fafatawa a wurare daban daban, haka ma kyakkyawar huldar aiki da wasu hukumomi ya taimaka gaya, za'a ci gaba da horas da jami'an tare da kula da sauyin jami'an da suka jima fagen daga suna fafatawa domin a tura sabbin jini"
Yanzu haka dai kwamandodjn mayakan na Najeriya na kan bitar ayukkan da suka gabatar a wannan shekara tare da sake kimtsawa da kara shirin fita fagen daga domin samar da tsaron kasa, abinda wasu ke fatar ganin an samu nasara. Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan aikin soji senata Ali Ndume yace akwai fatar ganin an samu nasara ga ayukkan sojin musamman jin irin kalaman da shugaban kasa yayi da kuma buda sashen kula da jiragen samarda rundunar sojin kasa.
Duba da har yanzu matsalar tana wanzuwa duk da wadannan tarin nasarori da ke bayyana ana samu, masanin tsaro kuma tsohon babban hafsan mayakan Najeriya Lt. Gen. Tukur Yusuf Buratai wanda rundunar sojin ta karrama tare da wasu mutane biyar yace lamarin samar da tsaro ba abu ne da za'a iya yi kai tsaye ba dole sai anyi hakuri kuma kowa na da gudunmuwar bayarwa ga samun nasarar sa.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5