Juma'ar nan rundunar sojan kasar Tailan ta gayaci tsohuwar Prime Ministar kasar Yingluck Shinawatra da wasu yan siyasa wani sansanin soja a birnin Bangkok.
WASHINGTON, DC —
Jiya Alhamis sojoji suka kwace mulki a wani juyin mulkin da ba'a zubar da jini ba, a yayinda Janaral Prayuth Chan Ocha yace sojoji sun dauki wannan mataki ne domin maido da bin doja da oda da kuma matsa lamba a kaddamar da sauye sauyen harkokin siyasa a kasar.
Rundunar soja ta jingine amfani da tsarin mulkin kasar ta kafa dokar hana fita daga karfe goma na darew zuwa biyar na asuba.
Haka kuma ta rufe kafofin yada labaru da dama.
Amirka da wasu kasashen yammacin duniya sunce juyin mulkin bai zama wajibi ba.
Yau Juma'a jakadan Amirka a kasar Thailand, Kristie Kanney ta fadawa Muryar Amurka cewa Amirka ta damu da matsayin kare hakki da 'yancin jama'a a kasar.
A wata sanarwar data gabatar yau juma'a. rundunar sojan Thailand tace an haramtawa wasu sannanun mutane dari da hamsin da biyar cikin harda hambararun shugabanin kasar barin kasar.