Muna Bukatar Gwamnati Ta Dauki Nauyin Ilimin 'Ya'yan Talakawa

Yau ya kasance yara yaran Afirka ranar da kungiyar hada kan Afirka ta AU ta ware domin tunawa da kisan gillar da aka yiwa wasu yara a Afirka ta Kudu

A shekarar 1976, daliba a Soweto a Afirka ta kudu zuka yi wani zanga zanga domin nuna rashin jindadinsu ga nuna wariyar launin fata wanda daga bisa yayi sanadiyar kashe wasu daga cikin daliban.

Kungiyar hada kan kasashen Afirka, ta ware 16, ga watan Yuni na kowace shekara domin tunawa da wannan ranarda kuma yin waiwaye ga matsalolin yaran Afirka.

Maryam Abubkar daya daga cikin yaran da wakilin muryar Amurka Hassan Umar Tambuwal, ya zanta dasu sun bukaci gwamnatin da ta taimakamasu da biyan kudaden makarantar da kuma abinci domin a cewarsu su ‘ya’yan talakawa ne.

Shima wani yaro dalibi mai suna Sani Daura, ya bukaci gwamnatin da ta hana sa yara aikin wahala kuma ta tallafawa yara talakawa da daukar nauyin iliminsu.

Your browser doesn’t support HTML5

Muna Bukatar Gwamnati Ta Dauki Nauyin Ilimin 'Ya'yan Talakawa - 4'03"