Mun Zo Lokacin Da Tattalin Arzikin Najeriya Ya Yi Kasa – Inji Gwamnan Jigawa

Gwamna Mohammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa, arewacin Najeriya

Gwamnan jihar jigawar Najeriya ya bayyanawa Mohammad Badaru Abubakar ya bayyana cewa yana iyakar kokarinsa a jihar don ganin an sami cimma biyan albashin ma’aikata mafi karanci duk da yake dai suna ta kokarin ci gaba da ayyukan raya jihar.

Ya bayyana cewa cewa za su ci gaba da biyan mafi karanci albashin. Yace duk da yake dai farashin man fetur a kasuwannin duniya ya fadi kuma ba wanda yasan ranar dawowarsa daidai. Gwamnan ya kara da cewa suna ta tsarin da kudin shigar jihar zai karu.

Inda yace suna ta kokarin jawo kamfanonin kasashen waje da masu zuba jari don su zo su kafa masana’antu a jihar a sami ayyukan yi. Game da maganar daya daga cikin kanfe din yakin neman zaben da jam’iyyar APC ta kudiri aniya na bawa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai ma ya yi magana.

Sai yace dama sun zo sun gaji mulkin da suka ga kananan hukumomin da cin gashin kansu. Ya bayyana cewa sun samu har asusun hadaka suke da shi da suke amfanin da shi wajen ayyukan ci gaban kasa. Sai dai ya koka akan yadda suka zo a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar ya sami babban gibi.

Ga dai yadda suka tattauna da abokin aikinmu Ibrahim Alfa Ahmed.

Your browser doesn’t support HTML5

Mun Zo Lokacin Tattalin Arzikin Najeriya Ya Yi Kasa Inji Gwamnan Jigawa - 4"43"