Mun Yi Wa Shugaba Biden Bayani Game Da Harbin Da Aka Yi A Pennsylvania-Mayorkas

Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump

Sakataren tsaron cikin gida na Amurka, Alejandro N. Mayorkas ya fitar da wata sanarwa game da harbin da aka yi a wurin yakin neman zaben tsohon Shugaban kasar Donald Trump a jihar Pennsylvania da safiyar yau.

A cikin sanarwar, Sakataren tsaron cikin gidan na Amurka Mayorkas ya bayyana cewa, "Ni da Daraktan ma'aikatar leken asiri Cheatle mun yi wa Shugaba Biden bayani game da harbin da aka yi yau a Pennsylvania. Ma'aikatar tsaron cikin gida (DHS) da Ma'aikatar Leken Asiri suna aiki tare da abokan aikinnmu, masu kula da kiyaye doka don gudanar da bincike kan harbin.

jami'an ba da kariya sun garzaya zuwa wurin Trump kuma an ci gaba da jin karar harbin yayin da jami’an ke kula da Trump.

Sanarwar ta kara da cewa, "Muna Allah wadai da wannan tashin hankalin da kakkausar murya tare da yaba wa hukumar leken asiri bisa matakin gaggawar da ta dauka a yau. Muna tare da Shugaba Biden, tsohon Shugaba Trump, da yakin neman zabensu, kuma muna daukar duk matakin da ya dace don tabbatar da tsaronsu. Kula da tsaron ’yan takarar Shugaban kasa da kuma taron yakin neman zabensu na daya daga cikin muhimman abubuwan da sashenmu ke ba da fifiko.”

Jami'an bada kariya yayin da suke iskewa da Trump daga filin taron yakin neman zabe

Tun farko Mai magana da yawun ma’aikatar leken asiri Anthony Guglielmi ya fitar da sanarwa a dandalin sada zumunta X, cewa, “Ma’aikatar leken asiri ta aiwatar da matakan kariya kuma tsohon Shugaban kasar yana cikin koshin lafiya. Yanzu haka Hukumar tana gudanar da bincike, ta kuma sanar da Hukumar Binciken manyan laifuka ta FBI."