Hakan a cewar shugaban hanya ce da ta taimaka wajen yaki da cin hanci da rashawa.
Mukaddashin shugaban hukumar tara kudaden shiga da rabasu a kasar Shetima Umar Abba yace samarda asusu daya ya taimaka wajen tara haraji da wasu kudaden gwamnati da ake tarawa da ba'a sani ba sai yanzu. Yanzu ana iya ganewa ba kamar da ba.
Saboda yawan asusun da ake anfani dasu da can da wuya a gano dukansu har a san abubuwan da aka biya cikinsu ba. Amma yanzu ana iya a san kudaden gwamnati da aka tara kama daga haraji zuwa kudin mai.
Masana tattalin arziki irin su Abubakar Ali na ganin tsarin zai fi yin nasara idan ya isa jihohi. Yace da farko mutane sun tsorata musamman cikin watanni biyun farko da zuwan mulkin Buhari amma yanzu an fara komawa gidan jiya. Abu na biyu a sake gina tsarin aikin ma'aikata ta yadda ko da Buhari ko babu Buhari ayyuka zasu tafi, ma'ana dokoki su yi aikinsu, kuma duk wanda ya saba masu a hukumtashi. Idan mutane na ganin ana daure mutum ko korarsa daga aiki saboda kaucewa ka'ida kowa zai tashi tsaye.
Yace yanzu Buhari ne kawai yake zancen canji. Ko cikin gwamnonin APC masu batun canji basu da yawa. Ko kudin da aka bayar a biya albashi akwai gwamnan da ya karkatar da nashi.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5