Mun Yi Gudun Gara Mun Fada Gidan Zago-Daliban Najeriya A Sudan

Daliban Najeriya suna kokarin isa kan iyaka bayan ficewa daga Khartoum

Daliban da aka kwaso daga makarantunsu a kasar Sudan inda ake fama da tashin hankali sun bayyana cewa, suna cikin mawuyacin halin kunci da tashin hankali a inda aka jibge su.

A hirar ta da Muryar Amurka, Zainab Usman Da’u da ke karatu a Jami’ar kasa da kasa ta Afrika da ake kira “International University of Africa” ta bayyana cewa, bayan tsaida shawarar fitar da su daga Sudan, motar da ta ke ciki da wadansu dalibai ta sami matsala, ta kafe a cikin yashin Hamada ba gida gaba, ba gida baya, inda suka shafe sama da sa’oi goma kafin aka iya fitar da mota suka ci gaba da tafiya.

Ta bayanna cewa, bayan sun shafe sa’oi suna tafiya, suka isa garin Alfa inda aka sauke su a wata tasha dake gefen hanya ba tare da yi masu wani bayani ba, sai dai kawai aka gaya masu cewa a nan tashar zasu fi iya samun abinci, duk da yake ba a yi masu wani tanadin abinci, ko kudin sayen abinci, ko kuma wurin kwana ba.

Daliban Najeriya suna kokarin isa kan iyaka bayan ficewa daga Khartoum

Zainab ta bayyana cewa, bisa ga bayanin da aka ayi masu, ofishin jakadancin Najeriya da ke Sudan ne ya tura motocin sufurin uku domin kwashe daliban kasar da ke Jami’ar. Tace, banda daliban da suka tashi tare a motoci uku daga makarantarsu, sun hadu da wadansu motocin biyu da su ma suka sauke daliban da suka kwaso a wannan tashar, abinda ya kai adadin daliban da suka isa tashar ranar kimanin 250, banda wadanda suka tarar a wurin da suka kai sama da dari biyar.

Dangane da yadda su ke samun abinci kuma, ta bayyana cewa, duk da yake akwai abinci a wurin, yana da tsada kwarai kuma galibin daliban da ke wurin kudinsu ya kare kasancewa babu wani jami’in gwamnatin Najeriya da ke tare da su, kuma ba a yi masu wani tanadi ko bayani kan mataki na gaba ba. Bisa ga cewarta, al’ummar unguwar da aka sauke su ne suka basu wadansu gine ginen da ba a kamala ba aka sauke mata. Ta kara da cewa, suna zaune ciki wani ginin ya rufta sai dai aka dace bai rutsa da kowa ba.

Daliban Najeriya suna kokarin isa kan iyaka bayan ficewa daga Khartoum

Dangane da lokacin da zasu ci gaba da tafiya zuwa kan iyaka, Zainab ta bayyana cewa, wadanda suka sauke su a garin da yake tazarar tafiyar minti talatin zuwa kan iyakar Sudan sun ce sai an kara masu kudi kafin su karasa da su zuwa kan iyaka.

Ku Duba Wannan Ma Najeriya Ta Tura Jirgin Sojin Sama Don Kwaso 'Yan Kasarta Da Suka Makale A Sudan

Saurari hirar Zainab da Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

Hira da Zainab Usman Da'u