Matakin ya biyo bayan wani taro da shugabannin ‘yan kasuwar su ka yi da shugaban hukumar yaki da cin hanci EFCC Abdulrasheed Bawa.
‘Yan kasuwar sun yi gangami da amfani da amsa kuwwa wajen sanar da dukkan ‘yan kasuwar matakin da su ka ce ba don wani matsin lamba ba ne daga wata hukuma ko kuma kai tsaye a alakanta da samame da jami’an EFCC su ka kai kasuwar a watan jiya.
Mukaddashin shugaban ‘yan kasuwar Alhaji Shehu Liman ya ce duba yanda dalar kan yi sanadiyyar tashin farashin kayan masarufi ya jawo su ka daidaita don ba da ta su gudunmawar da za ta kawo sauki.
Tuni wasu daga fitattun ‘yan kasuwar da su ka hada da Alhaji Murtala Bashir su ka mika wuya ga matakin.
Shin wannan matakin zai iya shafar sauran manyan kasuwannin canji na Kano, Lagos, Fatakwal, Enugu da sauran su?
Alhaji Shehu Liman ya ce Abuja ce cibiya kuma nan take matakin da a ka dauka a birnin kan karade sauran sassa na kasa.
Liman ya ce za su rika bitar farashin dalar a duk mako don kara daukar matakan sauko da ita daga tashin gauron zabi har sai ta daidaita sahu da farashin gwamnati.
Za a zuba ido a ga tasirin matakin da ba shakka zai samu turjiya daga ‘yan jari hujja da kan amfana da tsadar wajen cin kazamar riba
Saurari rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5