Mumunar tarzoma ta sake kunno kai a wasu yankuna na kudancin Philippines, duk da yarjejeniyar yancin cin gashin kai da aka kulla da wasu kungiyoyin musulmai. Hukumomi suna hangen ta’adancin daga kungiyoyin siyasan da basu sa hannu akan yarjejeniyar ba.
A karshen watan Augusta da farkon watan satumba, an samu hare haren bam har sau biyu a lardin Sultan Kudarat dake kudancin philippines, inda daya daga cikin harin ya hallaka mutane 2, 30 kuma sun rautana.
Rihottanin cikin gida sun bayyana cewa harin na biyu ya kashe mutane ukku ya kuma jikkata mutane bakwai bayan da bam din ya tarwatshe a garin Santos inda yabar mutane da fargabar tunanin harin zai iya dunga afkuwa akai akai.
Wannan harin ya faru ne bayan shekaru da dama ana rikici a tsiribin Mindanoa inda mutane 1,200 suka mutu a dalilin fada tsakanin yan tawaye musulamai da suke son Karin albarkatun a yankin su da Kiristoci masu rinjaye ke iko da su.