Girgizar kasar, wacce ta kai 6.4 a ma'aunin girgizar kasa, ta auku ne da safiyar yau dinnan Talata.
WASHINGTON D.C. —
Girgizar kasa mai karfin gaske ta abka ma wasu sassan babban birnin kasar Albania da safiyar yau dinnan Talata, wadda ta kashe a kalla mutane shida tare da raunata daruruwa.
Hukumar binciken girgizar kasa ta Amurka ta ce girgizar kasar ta kai girman 6.4 a ma'aunin girgizar kasa, wadda kuma tsakiyarta ke da nisan kilomita 30 arewa maso yamma da babban birnin kasar, wato Tirana.
Masu aikin ceto sun yi aiki don nemowa da kuma ceton mutane daga gine-ginen da suka lalace.
Mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaro ta ce an gano gawar mutane uku a cikin wani rusasshen gini a cikin garin Durres.