Mukarraban Gwamnan Taraba Suntai Sun Hakikance Ya Samu Lafiya

Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai.

Mr. Emmanuel Bello tsohon kwamishanan yada labarai wanda yake kan gaban a dawo da Gwamnan Danbaba Suntai yace ya samu sauki kuma kwanan nan zai koma bakin aikinsa.

Mr Bello yayi fatali da masu cewa gwamna Danbaba Suntai ba zai iya aikin gwamna ba.

Kamar yadda ya fada yace gwamna Suntai ya dawo daga jinya kuma kowace rana yake son ya koma aiki zai koma. A cikin tsarin mulkin kasar Najeriya idan gwamna ya dawo daga jinya zai gayawa majalisar dokokin jihar kana ya koma bakin aikinsa. Baya bukatar wani ya bashi izinin ya koma aiki.

Da wakilin Muryar Amurka ya tambayi Mr Bello ko yaushe mutanen Taraba zasu san ranar da gwamnan zai kama aikinsa sai yace yayi doguwar tafiya kuma akwai abubuwa da zai yi a Abuja kafin ya karasa Taraba. Akwai abokanansa da zasu ganshi da kuma gyara da yakamata suyi. Bayan ya kammala abun da ya keyi a Abuja zai koma Jalingo.

Dangane da cewa gwamnan ya dawo daidai lokacin da majalisar zartaswar jihar ta bukaci majalisar dokoki ta binciki lafiyarsa sai Mr. Bello yace lamarin ya bashi mamaki domin shi mukaddashin gwamnan Umar Garba ya je tashar jirgi wurin tarbar gwamnan. Abun mamaki ne a ce ranar Laraba mukaddashin gwamnan yace gwamnan bashi da lafiya amma ranar Asabar sai ya tafi tarbarsa.

To sai dai Bako Benjamin shugaban cigaban al'ummar Jukun na kasa yace yanzu Taraba tana zaman dar dar. Koina ana yin rikici. Yace yayin da yake magana da wakilin Muryar Amurka an kawo gawarwaki guda goma sha daya daga wani kauye Tunari zuwa cikin Wukari. Yanzu Wukarin ta rikice.Jihar Taraba ta rabu biyu tsakanin Musulmai da Kiristoci. Ba binciken lafiyar gwamnan ya damu talakawa ba yanzu. Duk fadi tashin da ake yi yanzu sabili da zaben 2015 ne.

Akan cancantar kafa kwamitin binciken lafiyar gwaman Barrister M.D. Mustapha masanin shari'a kuma dan siyasa yace bisa ga kundun tsarin mulkin kasa majalisar zartsawa nada hurumin ta bukaci majalisar dokoki ta kafa kwamitin likitoci kwararru biyar su binciki lafiyar gwamnan. Su ne zasu rubuta rahoto su ba majalisar.

'Yan majalisar dokokin jihar Taraba basu ce komi ba tukunna ganin cewa yanzu haka basa kasar suna Ingila kamar yadda Daniel Gani kakakin yada labaran majalisa ya shaida. Yace su basu samu wani sako ba domin majalisar tana hutu.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz

Your browser doesn’t support HTML5

Mukarraban Gwamnan Taraba Suntai Sun Hakikance Ya Samu Lafiya - 5' 41"