Mukaddashin shugaban yana magana ne a ranar iyaye maza ta duniya inda ya kira mijami'u su sanya ido ga masu rayuwa fiye da abun da ya dace su rika samu saboda hakan kan faru ne idan mutum na zarmiya.
Farfasa Osinbajo yace mutane su guji sata ko zarmiya a mijamiu saboda wasu da kan karbi albashi daidai da ma'aikatan gwamnati amma sun mallaki gidaje koina. Yace ya dace a tuhumi irin wadannan mutanen.
Yana mai cewa wasu idan an tambayesu dalilin da ya sa suke sata sai su ce wai domin su samu kudin yin kemfen nan gaba. Yace wannan karya ce karara.
Tsohon shugaban reshen matasa na kungiyar kiristocin Najeriya Pastor Samuel Donli yace za'a cin ma nasarar yaki da almundahana da rashin salama ta hanyar taimakawa kungiyoyin addini ko jan shugabannin addini a jika. Yace irin makudan kudaden da gwamnati ke kashewa kan tsaro idan suna taimakawa kungiyoyin addini suna shirya wasu ayyukan horaswa da fadakar da kawuna za'a samu masalaha da sauki. Ya ce ba sai sun jira turawa suna zuwa daga kasashen waje suna taimaka masu da kudi ba. Yace ya kamata Najeriya tayi da kanta domin zaman lafiyar al'ummarta.
A ra'ayin mai sharhi kan lamuran shari'a Yusuf Sallau Mutum Biyu yace sai gwamnati ta zuba ido akan bangarori ne za'a dawo da rikon amana. Amma yace hukumomin gwamnati ba sa samun kwararan hujjoji kafin gurfanar da mutum a kotu. EFCC suna kuskure kuma ba sa shirya ayyukansu kafin su je kotu.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5