Yace matsalar ita ce yadda ake yin anfani da kudin domin ko lokacin da ake da wadata a kasar gwamnatocin lokacin basa iya biyan albashi saboda suna watanda da kudi jama'a.
Yace a tarihin kasar cikin kankanin lokaci gwamnatinsu ta tabbatar da ana biyan ma'aikata akai akai harta a jihohi. Kudaden da gwamnatin tarayya ta rabawa jihohi na cikin kokarin biyan ma'aikata.
Bayan shugabannin kungiyar kwadago sun gana da mukaddashin shugaban kasa, Ayuba Wabba shugaban kungiayar kwadago yace suna son yakin da ake yi da cin hanci da rashawa ya cigaba saboda kasar tamkar ta zama kaman aljihun da ya huje. Ana zuba kudi cikinsa suna zubewa. Sun kira gwamnatin tarayya ta sa ido a jihohi domin nan ne ma'akata suka fi shan wahalar rashin biyan albashi.
Amma wani bangaren kungiyar 'yan kwadagon ya bayyana gangamin na NLC tamkar cin amanar kasa. Nasiru Kabir sakataren tsare tsare na kungiyar ULC yace sun hana mambobinsu shiga gangamin saboda cin amana ne na kasa. Yace maganar albashi sun gabatarwa gwamnati kokensu kuma an dauki mataki. Maganar tsadar rayuwa gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai duba lamarin. Nasiru yace tunda aka kirasu aka gaya masu abun da gwamnati keyi kamata yayi su tsaya su gani.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5