Kamar yadda aka saba duk shekara ana sadaukar da mako guda domin nazari kan muhimmancin kafofin sada zumunta a birnin Legas, wannan karon an shirya za a gudanar da shirin daga ranar 27, ga watan Fabarairu zuwa 3, ga watan Maris.
Domin nazarin muhimmancin kafofin sada zumunta akan shirya taruka wadanda ke hadawa da shugabanni da masu ruwa da tsaki da kuma sauran al’ummar kasa, don tattauna batun yadda kafofin sadarwa ke taimakawa, ko ke shafar kamfanoni da ma’aikatan gwamnati da kuma al’ada.
Taken taron na wannan shekarar zai mayar da hankali kan sabon salon yin amfani da fasaha da kuma makomar kafar sadarwa a Afirka.
Tarukan zasu duba yadda ake amfani da manhajojin dake baiwa mutane damar yada hotunan bidiyo a yanar gizo da kafofin da ake amfani da su wajen aikewa da sakonni ko kafe labarai shafukan yanar gizo, don samar da sahihiyar hanyar amfani da su don ci gaban al’ummar nahiyar Afirka.
Your browser doesn’t support HTML5