A wata hira da kakakin hukumar zaben Najeriya ta INEC, Aliyu Bello ya yi da wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka, Nasiru Adamu El Hikaya, ya zayyana mai wasu muhimman batutuwa da suka shafi yadda ya kamata masu kada kuri’a su yi zabe.
VOA: Karfe nawa za a bude rumfunan zabe kuma karfe nawa za a rufe?
INEC: Za a bude rumfunan zabe da misalin karfe 8 na safe za a ci gaba da hidimar zabe har zuwa karfe 2 na rana. Da karfe biyu, ana son rufe rumfunan zabe, har sai dai idan akwai mutane akan layi, nan ake da dalilin ci gaba da jefa kuri’a har ya zuwa mutum na karshe. Muddin karfe 2 ta samu mutum a wajen layi, bai hau layi ba, ba shi da ikon hawa layi sai dai ya jira zaben gaba.
VOA: Da wane yatsa ya kamata mutum ya dangwala kuri’arsa?
INEC: An bukaci duk mai yatsu ya yi amfani da babban yatsansa ya jefa kuri’a, wanda kuma ba shi da babban dan yatsa zai iya amfani da kowanne yatsa a cikin yatsun da Allah ya huwace masa.
VOA: Me ke bata kuri’a?
INEC: Duk wanda ya dangwala sama da gida daya a kuri’a daya, kuri’arsa ta lalace ba za ta yi tasiri ba, hakan nan duk wanda aka ba shi kuri’a ya dawo da ita bai dangwala a kowacce gida ba, kuri’ars ba za ta yi amfani ba.
Saurari karashen hirar domin samun cikakken bayani:
Your browser doesn’t support HTML5