A jumma’ar nan shekara ta 2021 miladiyya ta ke kawo karshe inda ya nuna asabar din nan ce za ta zama daya ga watan Janairun sabuwar shekara ta 2022.
Shekarar da ta dauki abubuwa da dama da su ka hada da fargabar karin farashin man fetur a Najeriya da hakan bai yiwu ba watakila sai a wannan sabuwar shekara.
Hakanan majalisar dokokin kasar ta amince da dokar sashin man fetur da ta sami sanya hannu daga sashen zartarwa; duk da haka dokar zaben ‘yar tinke na fidda ‘yan takara da tura sakamakon zabe ta na’ura ba ta kai labari ba don shugaba Buhari ya ki amincewa da ita.
Wani abu mai daukar hankali shi ne rufe layukan sadarwa da a ka yi a jihohin arewa maso yamma da ke fama da ayukan ‘yan bindiga don hakan ya zama hanyar rage karfin barayin mutane.
Hakan dai bai yi tasiri na zahiri ba don an cigaba da sacewa da ma kona mutanen da ran su.
A shekarar ce a ka cafke shugaban ‘yan awaren Biyafara Nnamdi Kanu daga kasar Kenya inda a ka dawo da shi Najeriya don fuskantar shari’ar cin amanar kasa da ta’addanci.
An kuma fuskanci abubuwan juyayi a yankin kudu maso gabashin kasar inda ‘yan aware kan kashe ‘yan arewa da ke sana’a a can da ma fille kan su ko babbaka su da wuta.
A Owerri na jihar Imo ma ‘yan bindigar sun yi kisan gilla ga tsohon mai ba wa shugaba Jonathan shawara kan siyasa Barista Ahmed Ali Gulak.
Hakazalika, a yankin Arewa matalar tsaro, kama daga kai hare-hare, kisan jama'a da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa ya zama ruwan dare, ba babba ba yaro ba mace ba namiji duk ba wanda ya tsira.
Fatan dai da ake shi shine sabuwar shekara ta 2022 ta zo da sauyi musamman ga sha'anin tsaro.