Muhimman Abubuwan Da Ke Gudana A Duniyar Tamaula

Kocin Kungiyar Real Madrid Zinade Zidane, ya ce dan wasan kungiyar Cristiano Ronaldo yana da koshin lafiya sosai kuma zai buga wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar turai 2018 wanda za su yi da Liverpool ranar 26 Mayu 2018.

Kocin ya bayyana haka sakamakon rade radin da ake yi na cewar dan wasan ya samu raunin da bazai iya fafatawa a wasan ba. Cristiano ya fice daga wasan da Real Madrid ta yi da babbar abokiyar hamayyar ta Barcelona inda aka tashi 2-2 a bangaren Laliga sakamakon doke shi da aka yi a idon sawunsa, Zidane ya ce hakan ba zai hana shi buga wasan karshe ba domin yana da karfin gwiwa har kashi 150 na fafatawa a wasan.

Zidane ya ce kuma ana tsammanin Dani Carvajal, da Isco zasu murmure dan fafatawa a wasan.

Cristiano ba zai buga wasan da Real Madrid zata yi da Sevilla ba a ranar laraba bangaren Laliga ba. Haka kuma ana tunanin ba zai buga wasa da Celta Vigo ba sai dai zai buga wasan karshe da zasu yi na Laliga da Villarreal.

Dan wasan baya na kungiyar kwallon Kafa ta Arsenal Laurent Koscielny, zai tafi jinya na tsawan watanni 6 sakamakon raunin da ya samu a tafin kafar sa a wasan da kungiyar ta yi tsakanita da Atletico Madrid na gasar Europe lig na dab da karshe zagaye na biyu inda aka doke Arsenal daci 1-0.

Laurent Koscielny, mai shekaru 32 ya fita daga wasan tun mintuna 12 da fara wasan, tuni dai Kocin kasar Faransa Didier Deschamps ya tabbabtar da cewar dan wasan ba zai buga wasan cin kofin duniya 2018 ga kasarsa ta faransa ba.

Shi ma dan wasan baya na Liverpool Joe Gomez, ba zai fafata a wasan karshe da kungiyar zata yi da Real madrid ba na cin kofin zakarun nahiyar turai 2018 wanda za a yi ranar 26/ Mayu 2018, sakamakon rauni da ya samu a gwiwar Kafarsa a wasan sada zumunci da ya buga wa kasarsa Ingila da tayi da kasar Netherlands a watan maris da ta gabata.

Your browser doesn’t support HTML5

Muhimman Abubuwan Da Ke Gudana A Duniyar Tamaula